Zabura 103:8 - Littafi Mai Tsarki8 Ubangiji mai jinƙai ne, mai ƙauna ne kuma, Mai jinƙirin fushi ne, cike yake da madawwamiyar ƙauna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.