Zan faɗi ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa, Zan yabe shi saboda dukan abin da ya yi mana. Ya sa wa jama'ar Isra'ila albarka mai yawa, Saboda jinƙansa da ƙaunarsa marar matuƙa.
Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim, Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu, Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki, Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.
Kakanninmu a Masar Ba su fahimci ayyukan Allah masu banmamaki ba, Sau da yawa sukan manta da irin ƙaunar da ya nuna musu, Suka tayar wa Mai Iko Dukka a Bahar Maliya.
Wane ne wannan da yake zuwa daga Bozara cikin Edom? Wane ne wannan da ya sha ado da jajayen kaya, yana tafe, ga shi kuwa ƙaƙƙarfa? Ubangiji ne, mai ikon yin ceto, yana zuwa ya yi sanarwar nasara.