Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.
Su rayayyun halittan nan huɗu kuwa, kowaccensu tana da fikafikai shida, jikinsu duk idanu ne ciki da waje, dare da rana kuwa ba sa daina waƙa, suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Ubangiji Allah Maɗaukaki, Shi ne a dā, shi ne a yanzu, shi ne kuma a nan gaba!”