4 Ba zan yi rashin aminci ba, Ba kuwa zan yi tunanin mugunta ba.
4 Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; ba abin da zai haɗa ni da mugunta.
Ubangiji yana ƙin masu muguwar niyya, amma yana murna da waɗanda suke aikata abin da yake daidai!
Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”
Sa'an nan zan ce musu, ‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugun aiki.’ ”
Kada ka yi abuta da mutane masu zafin fushi, ko masu zafin rai.
Ka rabu da ƙungiyar jahilai, ka rayu, ka bi hanyar ilimi.”
Ƙin mugunta shi ne tsoron Ubangiji, Na ƙi girmankai, da fāriya, da mugayen hanyoyi, Da maganganu na ƙarya.
Ku rabu da ni, ku masu zunubi! Zan yi biyayya da umarnan Allahna.
gama Ubangiji yana ƙin mutanen da suke aikata mugunta, amma yakan rungumi adalai ya amince da su.
Ku tafi daga nan, ku masu aikin mugunta! Ubangiji yana jin kukana.
amma sai aka zura ni a cikin babban kwando ta tagar garu, na kuɓuce masa.
Ba na tarayya da mutanen banza, Ba abin da ya gama ni da masu riya.
Ina ƙin tarayya da masu mugunta, Nakan kauce wa mugaye.
Mutum marar gaskiya abin ƙyama ne ga adali, adali kuma abin ƙyama ne ga mugun.