Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce, Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah, Ina bishe su a jere. Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa, Suna ta da murya, suna yabon Allah.
Ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza tare da Lawiyawa waɗanda suke zaune cikinku tun da yake ba su da rabo ko gādo tare da ku.
Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allahnku a inda Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya tabbatar da sunansa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawen da suke zaune a garinku, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.
Sai ku yi murna a cikin idin, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawe, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.
A rana ta takwas ya sallami jama'ar, su kuwa suka yabi sarki. Sa'an nan suka kama hanyar gidajensu suna murna, suna farin ciki saboda dukan alherin da Ubangiji ya yi wa bawansa, Dawuda, da jama'arsa, Isra'ilawa.
Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi kashi, ko wanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima a ƙofofin Ubangiji, don su yi godiya da yabo.
Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.