1 Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji!
1 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.
Ku raira waƙa ta farin ciki ga Ubangiji. Dukanku waɗanda suke a duniya, Ku yabe shi da waƙoƙi, kuna ta da murya da ƙarfi, Saboda farin ciki!
Da ya zo gab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu'ujizan da suka gani.
Ki raira waƙa da ƙarfi, ya ke Sihiyona! Ki ta da murya, ya Isra'ila! Ki yi murna, ki yi farin ciki, Ya ke Urushalima!
Dukanku adalai, ku yi murna, Ku yi farin ciki, Saboda abin da Ubangiji ya yi! Dukanku da kuke yi masa biyayya, Ku yi sowa ta farin ciki!
Har wa yau kuma an ce, “Ya ku al'ummai, ku yi ta farin ciki tare da jama'arsa.”
Ku yabi Allah da babbar murya ta farin ciki, Ya jama'a duka!
“Ya ku al'ummai, ku yabi jama'arsa, Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu, Zai ɗauki fansa a kan magabtansa, Zai tsarkake ƙasar jama'arsa.”
Zan yi shelar girmanka, ya Allahna, Sarkina, Zan yi maka godiya har abada abadin.
Ku yi tāfi saboda farin ciki, Ya ku jama'a duka! Ku raira waƙoƙi da karfi, ku yabi Allah!
A ranar, Ubangiji zai zama Sarkin Duniya duka, zai kuma zama shi ne Ubangiji shi kaɗai, ba wani suna kuma sai nasa.
Da ma sauran al'umma su yi murna, su raira waƙa ta farin ciki, Domin kana yi wa jama'a shari'a ta adalci, Kana kuma bi da dukan sauran al'umma.
Duk wanda yake a duniya, yana yi maka sujada, Yana raira maka waƙar yabbai, Yana raira yabbai ga sunanka.”
Allah ya hau kan kursiyinsa! Aka yi ta sowa ta murna, ana ta busa ƙahoni, Lokacin da Ubangiji yake hawa!
Ku raira waƙa ga Allah, ku mulkokin duniya, Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,