Ƙwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun, sai ya ƙone a wutar marar kasuwa.”
Al'ummai sun ci gaba kamar sukuwar raƙuman ruwa, amma Allah ya tsauta musu suka kuwa janye, aka kora su kamar ƙura a gefen dutse, kamar kuma tattaka a cikin guguwa.
Don haka za su zama kamar ƙāsashin da akan yi da safe, Ko kuwa kamar raɓa mai kakkaɓewa da wuri. Za su zama kamar ƙaiƙayi wanda ake shiƙarsa cikin iska a masussuka, Ko kuwa kamar hayaƙin da yake fita ta bututu.
Ya Urushalima, dukan baƙin da suka auka miki da yaƙi za a hure su kamar yadda iska take hure ƙura, sojojinsu kuma masu firgitarwa za a hure su kamar yadda iska take hure tattaka. Farat ɗaya ba zato ba tsammani,