Amma Allah ya ce masa, “Daidai ne ka yi fushi saboda 'yar kurangar?” Yunusa ya amsa, “Hakika, daidai ne a gare ni in yi fushi, har ma in yi fushin da ya isa in mutu!”
Ahab ya koma gida da baƙin ciki da rai a ɓace saboda abin da Nabot Bayezreyele ya faɗa masa. Ahab ya kwanta a gadonsa, ya mai da fuskarsa bango ya ƙi cin abinci.