Amma Allah ya ce masa, “Daidai ne ka yi fushi saboda 'yar kurangar?” Yunusa ya amsa, “Hakika, daidai ne a gare ni in yi fushi, har ma in yi fushin da ya isa in mutu!”
To, da Bafarisiyen da ya kira shi ya ga haka, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce, da kuma ko wace irin mace ce wannan da yake taɓa shi, don mai zunubi ce.”
Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al'ummai.