Yunana 1:5 - Littafi Mai Tsarki5 Dukan matuƙan jirgin suka firgita, sai kowannensu ya shiga roƙon allahnsa. Suka yi ta jefar da kayan da suke cikin jirgin a ruwa don su sami sauƙi. Yunusa kuwa yana can cikin jirgi, a kwance, yana ta sharar barci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Dukan matuƙan jirgin suka tsorata, kowannensu kuma ya yi kuka ga allahnsa, suka kuma jefar da kayan jirgi a cikin teku domin su rage nauyin jirgin. Ana cikin haka, ashe, Yunana ya sauka can ƙarƙashin jirgi ya je ya kwanta, yana ta sharar barcinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |