Suka je suka tashe shi, suka ce, “Maigida, Maigida, mun hallaka!” Ya farka, ya tsawata wa iskar da kuma haukan ruwa. Sai suka kwanta, wurin ya yi tsit.
Aka binne ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan a kabarin Kish, tsohon Saul, a Zela a ƙasar Biliyaminu. Aka aikata dukan abin da sarki ya umarta. Bayan haka Allah ya ji addu'arsu a kan ƙasar.