Yunana 1:12 - Littafi Mai Tsarki12 Yunusa ya ce, “Sai ku ɗauke ni ku jefa ni cikin tekun, sa'an nan hadirin zai lafa. Gama na sani saboda ni ne wannan hadiri mai banrazana ya auko muku.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Ya amsa musu ya ce, “Ku ɗauke ni ku jefa a cikin teku, tekun zai kwanta. Na san cewa laifina ne ya jawo wannan babban hadirin da ya auka muku.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dawuda ya ce wa Allah, “Ai, ni ne na ba da umarni a ƙidaya jama'ar. Hakika, ni na yi zunubi, na kuwa aikata mummunan abu, amma waɗannan talakawa fa, me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, ka bar hannunka ya yi gāba da ni da gidan tsohona, amma kada ka yi gāba da jama'arka, har da za ka aukar musu da annoba.”