Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yowel 3:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Su bubbuge allunan garmunansu, Su yi takuba da su. Su ƙera māsu da wuƙaƙen da ake yi wa itatuwa aski. Sai marar ƙarfi ya ce, “Ni jarumi ne!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ku bubbuge garemaninku su zama takuba da kuma laujenku su zama māsu. Bari raunana su ce, “Ni mai ƙarfi ne!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yowel 3:10
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A ranar, Ubangiji zai kiyaye mazaunan Urushalima, har wanda yake marar ƙarfi a cikinsu zai zama mai ƙarfi kamar Dawuda. Jama'ar Dawuda za ta zama kamar Allah, kamar mala'ikan Ubangiji a gabansu.


Amma idan ka zaci ta wannan hanya ce za ka zama da ƙarfi don yaƙi, Allah zai kā da kai a gaban maƙiyi, gama Allah yana da iko ya yi taimako, ko kuwa ya ƙi.”


Zai shara'anta tsakanin al'umman duniya masu yawa, Zai sulhunta jayayyar da take tsakanin manyan al'ummai, Za su mai da takubansu garemani, Māsunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace. Al'umma ba za ta ƙara fita zuwa yaƙi ba, Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.


Zai sulhunta jayayyar da yake tsakanin manyan al'ummai, Za su mai da takubansu garemani, Masunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace, Al'ummai ba za su ƙara fita zuwa yaƙi ba, Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.


Ya ce musu, “Amma a yanzu duk mai jakar kuɗi yă ɗauka, haka kuma mai burgami. Wanda kuwa ba shi da takobi, ya sayar da mayafinsa ya saya.


Ku wasa kibau, ku cika kwaruruwanku! Ubangiji ya ta da ruhun sarakunan Mediyawa, Domin yana niyyar hallaka Babila. Gama Ubangiji zai yi ramuwa saboda Haikalinsa.


Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, “Uwargida, an raba ki da rashin lafiyarki!”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ