Yowel 2:20 - Littafi Mai Tsarki20 Zan kawar muku da waɗanda suka zo daga arewa, Zan kori waɗansunsu zuwa cikin hamada. Zan kori sahunsu na gaba zuwa cikin Tekun Gishiri, Zan kori sahunsu na baya, zuwa cikin Bahar Rum. Gawawwakinsu za su yi ɗoyi. Zan yi musu haka saboda dukan abin da suka yi muku.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202020 “Zan kori sojojin arewa nesa da ku, in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma, kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin teku da kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum. Warinsu kuma zai bazu; ɗoyinsu zai tashi.” Tabbatacce ya yi al’amura masu girma. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |