Yowel 2:13 - Littafi Mai Tsarki13 Ku kyakkece zuciyarku, ba tufafinku kaɗai ba.” Ku komo wurin Ubangiji Allahnku. Gama shi mai alheri ne, mai jinƙai, Mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, Yakan tsai da hukunci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Ku kyakkece zuciyarku ba rigunanku ba. Ku juyo ga Ubangiji Allahnku, gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma mai jinkirin fushi da yawan ƙauna, yakan kuma janye daga aika da bala’i. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.