Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yowel 1:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Ku sa a yi azumi, Ku kira muhimmin taro. Ku tara dattawa da dukan mutanen ƙasar A Haikalin Ubangiji Allahnku, Ku yi kuka ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Ku yi shelar azumi mai tsarki; ku kira tsarkakan taro. Ku kira dattawa da kuma dukan mazaunan ƙasar zuwa gidan Ubangiji Allahnku, ku kuma yi kuka ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yowel 1:14
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai dukan mutane da dabbobi su sa tufafin makoki. Kowa ya roƙi Allah da gaske, kowa kuma ya bar mugayen ayyukan da yake yi.


A sa'an nan kuwa mutanen Yahuza suna tsaye a gaban Ubangiji, su da ƙananansu, da matansu, da 'ya'yansu.


A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. A rana ta takwas kuma sai su yi muhimmin taro na sujada, su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Rana ce ta yin sujada, kada su yi aiki.


Kowace rana, tun daga rana ta fari zuwa rana ta ƙarshe, Ezra yakan karanta musu daga cikin littafin dokokin Allah. Suka kiyaye idin har kwana bakwai. A rana ta takwas kuma suka muhimmin taro bisa ga ka'ida.


Yehu kuma ya sa a yi muhimmin taro saboda Ba'al. Aka kuwa kira taron,


“Ka tattara dukan Yahudawan da suke a Shushan, su yi domin, kada su ci ko su sha dare da rana, har kwana uku. Ni kuma da kuyangina za mu yi haka nan. Sa'an nan zan tafi wurin sarki, ko da yake ba bisa ga doka ba, idan na halaka, na halaka ke nan.”


A watan tara a shekara ta biyar ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, sai dukan jama'ar Urushalima da dukan jama'ar da suka zo Urushalima daga biranen Yahuza suka yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji.


Ku dattawa, ku kasa kunne, Bari kowa da kowa da yake cikin Yahuza, ya kasa kunne. Wani abu mai kamar wannan ya taɓa faruwa a lokacinku, Ko a lokacin kakanninku?


Sai mutanen Nineba suka gaskata Allah, suka tsai da shawara, cewa kowa da kowa ya yi azumi. Dukan mutane kuwa babba da yaro, suka sa tufafin makoki.


Ya ke al'umma marar kunya, ku tattaru, ku yi taro,


“Yahuza tana makoki, Ƙofofin biranenta suna lalacewa, Mutanenta suna kwance a ƙasa, suna makoki, Urushalima tana kuka da babbar murya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ