Yoshuwa 9:9 - Littafi Mai Tsarki9 Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Suka amsa suka ce, “Bayinka sun zo ne daga ƙasa mai nisa gama Ubangiji Allahnka ya yi suna sosai. Gama mun ji labarin abubuwan da ya yi. Dukan abubuwan da ya yi a Masar အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu. “Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al'ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al'ummai.
Waɗannan Lawiyawa kuma, wato Yeshuwa, da Kadmiyel, da Bani, da Hashabnaiya, da Sherebiya, da Hodiya, da Shebaniya, da Fetahiya su ne suka yi kiran sujada, suka ce, “Ku miƙe tsaye, ku yabi Ubangiji Allahnku, Ku yabe shi har abada abadin. Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka, ya Ubangijii, Ko da yake ba yabon da ɗan adam zai yi har ya isa.”