sai suka yi musu hila, suka shirya guzuri, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu, sun kuwa sha ɗinki.
Ya zama fa a wannan shekara, a watan biyar, a shekara ta huɗu ta sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza, sai annabi Hananiya ɗan Azzur mutumin Gibeyon, ya yi magana da ni a Haikalin Ubangiji, a gaban firistoci da dukan jama'a, ya ce,
Da Adonizedek, Sarkin Urushalima, ya ji yadda Joshuwa ya ci Ai, har ya hallakar da ita sarai kamar yadda ya yi wa Yariko da sarkinta, da kuma yadda mazaunan Gibeyon suka yi amana da Isra'ilawa, har suna zama cikinsu.
A wannan rana kuwa Joshuwa ya ci Makkeda da yaƙi, ya kashe mutanenta da sarkinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Ya yi wa Sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa Sarkin Yariko.
Ubangiji ya bashe ta da sarkinta a hannun Isra'ilawa, suka kuwa buge ta da takobi, da kowane mutum da yake cikinta, ba su rage kowa cikinta ba. Suka yi wa sarkinta kamar yadda suka yi wa Sarkin Yariko.
Sa'an nan Sulemanu da dukan waɗanda suke tare da shi, suka tafi masujadar da take a Gibeyon, gama alfarwar sujada ta Allah, wadda Musa, bawan Ubangiji ya yi a jeji, tana can.