Amma Abram ya ce wa Saraya, “Ga shi, baranyarki tana cikin ikonki, yi yadda kika ga dama da ita.” Saraya ta ƙanƙanta ta, sai Hajaratu ta gudu daga gare ta.
Na yi fushi da mutanena, Na maishe su kamar su ba nawa ba ne. Na sa su a ƙarƙashin ikonki, Ba ki kuwa yi musu jinƙai ba, Har da tsofaffi ma kin ba su wuya.
Sa'an nan ya zo wurin mutanen Sukkot ya ce musu, “To, ga Zeba da Zalmunna waɗanda kuka yi mini ba'a saboda su, kuna cewa, ‘Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka da suka gaji abinci?’ To, ga su!”
Sai wakilin gidan, da wakilin birnin, da dattawa, da masu lura da 'ya'yan sarki, suka aika wurin Yehu suka ce, “Mu barorinka ne, duk abin da ka umarce mu, za mu yi. Ba za mu naɗa wani sarki ba, sai ka yi duk abin da ka ga ya yi maka kyau.”