Za ku gina mini bagade na ƙasa. A kansa za ku miƙa mini hadayu na ƙonawa da na salama, da tumakinku da shanunku. A duk inda na sa a tuna da sunana zan zo wurinku in sa muku albarka.
Nuhu ya gina wa Ubangiji bagade, ya ɗiba daga cikin kowace irin dabba mai tsarki, da kowane tsuntsu mai tsarki, ya miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden.