Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 7:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Sai Joshuwa ya ce, “Don me ka wahalshe mu? Kai ma, Ubangiji zai wahalshe ka yau!” Dukan Isra'ilawa suka jajjefe su da duwatsu, suka ƙone su da wuta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Yoshuwa ya ce, “Me ya sa ka jawo mana wahala haka? Ubangiji zai kawo maka wahala kai ma a yau.” Sai dukan Isra’ilawa suka jajjefe shi, bayan da suka gama jifarsa sai suka ƙone sauran.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 7:25
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma sai ku tsare kanku daga abubuwan da aka haramta don a hallaka su. Kada ya zama bayan da kuka haramta su ku sāke ɗaukar wani abu daga cikinsu, har da za ku sa zangon Isra'ilawa ya zama abin hallakarwa, ku jawo masa masifa.


Karmi shi ne mahaifin Akan wanda ya jawo wa Isra'ila wahala a kan abin da aka haramta.


to, ku kawo macen, ko mutumin, da ya aikata wannan mugun abu a bayan ƙofar garinku, nan za ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.


“Fito da wanda ya yi saɓon nan daga cikin zangon. Ka kuma sa dukan waɗanda suka ji shi su sa hannuwansu a bisa kansa. Taron jama'ar kuwa su jajjefe shi da duwatsu.


ya ce wa mutanen Isra'ila, “Duk Ba'isra'ile da kowane baƙo da yake zaune cikin Isra'ila, wanda ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga Molek, lalle ne a kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi da duwatsu.


Ku kula fa, kada kowa yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka,


domin kuwa Allah ya ga adalci ne, yă yi sakamokon ƙunci ga waɗanda suke ƙuntata muku,


Da ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su mai da kansu babanni!


Zai zama kuwa wanda aka same shi da haramtattun abubuwa, za a ƙone shi da wuta, shi da dukan abin da yake da shi, domin ya tā da alkawarin Ubangiji, ya kuma yi abin kunya cikin Isra'ila.’ ”


Sa'an nan, sai mutanen garin su jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. Dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro.”


Ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, saboda ya yi niyyar janye ku daga bin Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta.


'Yar firist wadda ta ɓata kanta da yin aikin karuwanci, ta ƙasƙantar da mahaifinta, sai a ƙone ta da wuta.


Duk mutumin da ya auri 'ya tare da mahaifiyarta, wannan mugun abu ne, shi da su biyu ɗin, sai a ƙone su da wuta, don kada mugun abu ya kasance a cikinku.


Bayan misalin wata uku, aka faɗa wa Yahuza, “Tamar surukarka ta yi lalata, har ma tana da ciki.” Sai Yahuza ya ce, “A fito da ita, a ƙone ta.”


Sai Yakubu ya ce wa Saminu da Lawi, “Kun jawo mini wahala. Kun sa na zama abin ƙi ga Kan'aniyawa da Ferizziyawa mazaunan ƙasar. Mutanena kima ne, in suka haɗa kai suka fāɗa mini, za su hallaka ni, da ni da gidana.”


Jonatan kuwa ya ce, “Lalle mahaifina ya wahalar da jama'a! Dubi yadda na wartsake sa'ad da na ɗanɗana 'yar zuman nan.


Da haka nan dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro, har da ba za su ƙara aikata mugun abu irin wannan a cikinku ba.


Yin fashi yakan zama sanadin mutuwar ɗan fashi a koyaushe. Wannan shi ne abin da yakan sami kowane mutum da ya kama sana'ar sata.


Mai ƙoƙarin cin ƙazamar riba yana jefa iyalinsa a wahala ke nan. Kada ka karɓi hanci, za ka yi tsawon rai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ