Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 7:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Tashi, ka tsarkake jama'a, ka ce, ‘Ku tsarkake kanku domin gobe, gama Ubangiji, Allah na Isra'ila ya ce akwai haramtattun abubuwa a tsakiyarku. Ya Isra'ila, ba ku iya tsayawa a gaban abokan gābanku ba, sai kun kawar da haramtattun abubuwa daga tsakiyarku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 “Tashi, ka je ka tsarkake mutane. Ka ce musu su tsarkake kansu, su yi shiri domin gobe; gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, a cikinku akwai abubuwan da aka keɓe, ya Isra’ilawa. Ba za ku iya yin tsayayya da abokan gābanku ba sai in kun rabu da abubuwan nan da aka haramta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 7:13
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Joshuwa ya ce wa jama'a, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai aikata abin al'ajabi a tsakiyarku.”


Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan'uwanka.


Isra'ilawa sun yi zunubi. Sun ta da alkawarina, wanda na umarce su, gama sun ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, sun sa a kayansu, sun yi ƙarya.


Amma sai ku tsare kanku daga abubuwan da aka haramta don a hallaka su. Kada ya zama bayan da kuka haramta su ku sāke ɗaukar wani abu daga cikinsu, har da za ku sa zangon Isra'ilawa ya zama abin hallakarwa, ku jawo masa masifa.


Yanzu kuwa kuna niyya ku mai da jama'ar Yahuza da ta Urushalima su zama bayinku mata da maza. Ashe, ku kanku ba ku da waɗansu zunuban da kuka yi wa Ubangiji Allahnku?


'Ya'yan Yakubu kuwa suka tarar da kisassun, suka washe birnin, saboda sun ɓata 'yar'uwarsu.


“Idan ɗan'uwanka, wato ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko 'yarka, ko ƙaunatacciyar matarka, ko amininka ya rarrashe ka a asirce, yana cewa, ‘Bari mu tafi mu bauta wa gumaka waɗanda ku da ubanninku ba ku san su ba,’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ