Ba mutumin da zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Kamar yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai, ba zan kunyatar da kai ba, ba kuwa zan yashe ka ba.
Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar,
Sa'ad da dukan sarakunan da suke hayin Urdun, na cikin ƙasar tuddai, da na ƙasar kwari a gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon, wato sarakunan Hittiyawa, da na Amoriyawa, da na Kan'aniyawa, da na Ferizziyawa, da na Hiwiyawa, da na Yebusiyawa, suka ji wannan labari,
Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.
Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.
Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”