Yoshuwa 5:7 - Littafi Mai Tsarki7 'Ya'yansu ne kuwa waɗanda Ubangiji ya tā da su a maimakonsu, su ne Joshuwa ya yi wa kaciya, gama ba su da kaciya, domin a hanya ba a yi musu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Sai ya sa yaransu ne suka taso a maimakonsu, su ne waɗanda Yoshuwa ya yi wa kaciya. Sun kasance ba kaciya gama ba a yi musu ba a hanya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Gama shekara arba'in Isra'ilawa suna ta tafiya a jeji, har dukan al'umma, har da mayaƙan da suka fito daga Masar, suka hallaka, domin ba su kula da muryar Ubangiji ba. A gare su kuwa Ubangiji ya rantse, ba zai bar su su ga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba su ba, ƙasar da take mai yalwar abinci.