Nebukadnezzar fa ya matso kusa da ƙofar tanderun gagarumar wuta, ya ce, “Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, bayin Allah Maɗaukaki, ku fito, ku zo nan!” Sai Shadrak, da Meshak, da Abed-nego suka fita daga cikin wutar.
Da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka fito daga tsakiyar Urdun, suka taka sandararriyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya malalo ya tumbatsa kamar dā.