Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 3:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari cewa, ‘Sa'ad da kuka shiga gefen ruwan Urdun, sai ku tsaya cik a wurin.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Ka ce wa firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, ‘Sa’ad da kuka kai bakin Urdun, ku shiga cikin ruwan ku tsaya.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 3:8
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A sa'ad da Isra'ilawa duka suna tafiya a kan sandararriyar ƙasa a cikin Urdun, firistoci kuwa waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka yi ta tsayawa a bisa sandararriyar ƙasa a tsakiyar Urdun har al'ummar ta gama hayewa.


suna umartar jama'ar suna cewa, “Sa'ad da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi,


Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa,


Ɗaya daga cikin 'ya'yan Yoyada ɗan Eliyashib, babban firist, surukin Sanballat ne, Bahorone, saboda haka sai na kore shi daga wurina.


Sai kuma na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu, su yi tsaron ƙofofin don a kiyaye ranar Asabar da tsarki. “Ya Allahna, ka tuna da wannan aiki nawa, ka rayar da ni saboda girman madawwamiyar ƙaunarka.”


Ikon Allah kuma yana kan Yahuza, ya ba su zuciya ɗaya ta su yi abin da sarki da sarakunansa suka umarta bisa ga maganar Ubangiji.


Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.


Sai Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawar a bisa bagaden. Sa'ad da aka fara miƙa hadaya ta ƙonawa, sai aka fara raira waƙa ga Ubangiji, aka busa ƙaho, sai sauran masu kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushe na Dawuda, Sarkin Isra'ila, suka kama.


Sai suka tattara 'yan'uwansu maza, suka tsarkake kansu, suka shiga bisa ga umarnin sarki, bisa ga maganar Ubangiji domin su tsabtace Haikalin Ubangiji.


Sai Musa ya ce wa jama'a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau.


Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “A yau ɗin nan zan fara ɗaukaka ka a gaban dukan Isra'ilawa domin su sani, kamar yadda na kasance tare da Musa, haka kuwa zan kasance tare da kai.


Joshuwa kuma ya ce wa Isra'ilawa, “Ku kusato ku ji zantuttukan Ubangiji Allahnku.”


Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni zuwa Kogin Urdun.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi tare.


Da jama'a duka suka gama hayewa, sai akwatin Ubangiji da firistocin suka wuce gaban jama'ar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ