Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 3:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ta haka ne za ku san cewa Allah mai rai yana tare da ku, kuma ba shakka a gabanku za ku gani zai kore Kan’aniyawa, Hittiyawa, Hiwiyawa, Ferizziyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa da Yebusiyawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 3:10
37 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da kuke shiga ku mallake ta, zai korar muku da al'ummai da yawa, su Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, al'umma bakwai ke nan, waɗanda suka fi ku yawa, da kuma ƙarfi.


Zan kuwa aiki mala'ika a gabanka. Zan kuma kori Kan'aniyawa da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Farizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.


Abu ne fa mai matuƙar bantsoro a fāɗa a cikin hukuncin Allah Rayayye.


Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?”


Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya, Shi Allah mai rai ne, Shi Sarki ne madawwami. Saboda hasalarsa duniya ta girgiza, Al'ummai ba za su iya jurewa da fushinsa ba.


Mai yiwuwa ne Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun da Rabshake ya yi wanda ubangidansa, Sarkin Assuriya, ya aiko don yi wa Allah mai rai ba'a. Bari Ubangiji Allahnka ya hukunta masa saboda maganganunsa, sai ka yi addu'a saboda sauran da suka ragu.”


Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa, “Yau mun sani Ubangiji yana tare da mu domin ba ku ci amanar Ubangiji ba.”


A wannan rana zan husata da su ƙwarai, in rabu da su, in ɓoye musu fuskata, za a cinye su. Masifu da wahalai za su same su. Za su kuwa ce a ranar, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu.’


don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.


Domin su da kansu suke ba da labarin irin ziyartarku da muka yi, da kuma yadda kuka rabu da gumaka, kuka juyo ga Allah, domin ku bauta wa Allah Rayayye na gaskiya,


“Duk da haka yawan mutanen Isra'ila Zai zama kamar yashi a bakin teku, Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba. Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’


Ubangiji ya bayyana kansa ta wurin shari'arsa mai adalci, Mugaye sun kama kansu da abubuwan da suka aikata.


Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu?


Sai Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Almasihu, Ɗan Allah Rayayye.”


Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.


Mikaiya kuwa ya ce, “In dai ka komo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana da ni ba.” Ya ƙara da cewa, “Kowa ya kasa kunne ga abin da na faɗa.”


Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alheri da ya yi wa gidan Isra'ila.


Sai aka sa wa wurin suna, “Masaha” da “Meriba”, saboda Isra'ilawa suka yi husuma, suka kuma jarraba Ubangiji suna cewa, “Ubangiji yana tare da mu, ko babu?”


Mu kuwa mun gaskata, mun kuma tabbata kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”


Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku, shi Allah ne mai girma, mai banrazana.


Joshuwa kuma ya ce wa Isra'ilawa, “Ku kusato ku ji zantuttukan Ubangiji Allahnku.”


Sa'ad da dukan sarakunan da suke hayin Urdun, na cikin ƙasar tuddai, da na ƙasar kwari a gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon, wato sarakunan Hittiyawa, da na Amoriyawa, da na Kan'aniyawa, da na Ferizziyawa, da na Hiwiyawa, da na Yebusiyawa, suka ji wannan labari,


Dawuda ya ce wa Ahimelek Bahitte, da Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab, “Wa zai tafi tare da ni zuwa sansanin Saul?” Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”


Ina jin ƙishinka, ya Allah, ya Allah Mai Rai, Yaushe zan tafi in yi sujada a gabanka?


da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Girgashiyawa, da kuma Yebusiyawa.”


Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan'aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.”


Ya kuma aika zuwa ga Kan'aniyawan da suke gabas da yamma, da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke ƙasar tuddai, da Hiwiyawa da suke zaune a gindin Dutsen Harmon a ƙasar Mizfa.


da ƙasar tuddai, da filayen kwaruruka, da kwarin Araba, da gangaren tuddai, da jejin, da Negeb, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.


Da kuka haye Urdun, kuka zo Yariko, mutanen Yariko kuwa suka yi yaƙi da ku, haka kuma Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Kan'aniyawa da Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, amma na ba da su a gare ku.


da Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ