Yoshuwa 24:7 - Littafi Mai Tsarki7 A sa'ad da suka yi mini kuka, na sa duhu a tsakaninsu da Masarawa, na sa teku ta shafe Masarawa. Da idonku kun ga abin da na yi wa Masar, kuka kuma zauna a jeji da daɗewa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Amma suka yi kuka ga Ubangiji don taimako, ya kuwa sa duhu ya raba tsakaninsu da Masarawa; ya sa teku ya rufe Masarawa. Kun gani da idanunku abin da na yi wa Masarawa, sa’an nan kuka zauna a jeji na tsawon lokaci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Gama shekara arba'in Isra'ilawa suna ta tafiya a jeji, har dukan al'umma, har da mayaƙan da suka fito daga Masar, suka hallaka, domin ba su kula da muryar Ubangiji ba. A gare su kuwa Ubangiji ya rantse, ba zai bar su su ga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba su ba, ƙasar da take mai yalwar abinci.