“Da ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya mutane za su ce, ‘Ni na Ubangiji ne!’ Za su zo su haɗa kai da jama'ar Isra'ila. Ko wanne zai ɗaura sunan Ubangiji a dantsensa, Ya ce da kansa ɗaya daga cikin mutanen Allah.”
Dukan jama'a kuwa suka amsa masa baki ɗaya, suka ce, “Dukan abin da Ubangiji ya faɗa za mu aikata.” Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama'ar suka bayar.
Yau kun shaida, cewa Ubangiji shi ne Allahnku, za ku yi tafiya cikin tafarkunsa, za ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da farillansa, za ku kuma yi masa biyayya.
Musa ya tafi, ya faɗa wa jama'a dukan dokokin Ubangiji da ka'idodinsa, sai dukan jama'a suka amsa gaba ɗaya, suka ce, “Za mu kiyaye dukan dokokin da Ubangiji ya ba mu.”