Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 24:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Gama Ubangiji Allahnmu ne ya fisshe mu da kakanninmu daga ƙasar Masar, a gidan bauta. Shi ne wanda ya aikata manyan alamu a idonmu, ya kuma kiyaye mu a dukan hanyar da muka bi, da cikin dukan al'umman da muka ratsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Ubangiji Allahnmu ne da kansa ya fitar da iyayenmu daga Masar, daga ƙasar bauta, ya yi manyan abubuwan al’ajabi, a idanunmu. Ya kiyaye mu cikin dukan hanyar da muka bi, da cikin ƙasashen da muka ratsa;

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 24:17
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

‘Kun dai ga abin da na yi da Masarawa, da yadda na ɗauke ku kamar yadda gaggafa take ɗaukar 'yan tsakinta, na kawo ku gare ni.


Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku, Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura. Ni na halice ku zan kuwa lura da ku, Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”


Jama'a kuwa suka amsa suka ce, “Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji, har a ce mu bauta wa gumaka.


Ubangiji kuwa ya kore mana dukan Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar, domin haka za mu bauta wa Ubangiji, gama shi ne Allahnmu.”


Musa ya ce wa jama'a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba.


In wata rana 'ya'yanku suka tambaye ku cewa, ‘Ina ma'anar wannan?’ Sai ku ce musu, ‘Da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar, daga gidan bauta.


Ku tuna kuma da wahalar da kuka gani da idonku, da alamu, da mu'ujizai, da dantse mai iko mai ƙarfi wanda Ubangiji Allahnku ya fito da ku. Haka nan kuma Ubangiji Allahnku zai yi da dukan al'umman nan da kuke jin tsoronsu.


Sai Musa ya kira dukan Isra'ilawa ya ce musu, “Ai, kun ga dukan abin da Ubangiji ya yi wa Fir'auna da barorinsa a dukan ƙasar Masar.


Gama rabon Ubangiji shi ne jama'arsa, Yakubu shi ne rabon gādonsa.


“Amma a gare mu, Ubangiji shi ne Allahnmu, ba mu kuwa rabu da shi ba. Muna da firistoci, 'ya'yan Haruna, maza, masu yi wa Ubangiji hidima, da Lawiyawa masu yi musu hidima.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ