Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 24:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Idan ba ku da nufi ku bauta wa Ubangiji, to, yau sai ku zaɓi wanda za ku bauta wa, ko gumakan da kakanninku suka bauta wa a wajajen hayin Kogin Yufiretis, ko kuma gumakan Amoriyawa waɗanda kuke zaune a ƙasarsu, amma ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 24:15
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Iliya kuwa ya zo kusa da jama'a ya ce, “Har yaushe za ku daina yawo da hankalinku? Idan Ubangiji shi ne Allah, to, ku bauta masa, in kuwa Ba'al ne Allah, to, ku bauta masa.” Mutane duk suka yi tsit, ba su ce uffan ba.


Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, ta koma ga bauta wa gumakan al'umman nan. Kada a iske wani tushe a cikinku mai ba da 'ya'ya masu dafi, masu ɗaci.


“Ya ku, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, bari kowa ya tafi ya bauta wa gunkinsa daga yanzu zuwa gaba, tun da yake ba za ku kasa kunne gare ni ba, amma kada ku ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku.


Da ya iso ya kuma ga alherin da Allah ya yi musu, ya yi farin ciki, ya gargaɗe su duka su tsaya ga Ubangiji da dukan zuciyarsu,


Ba za ku rusuna wa allolinsu ba, balle fa ku bauta musu, kada ku yi yadda suke yi. Sai ku hallaka allolinsu ɗungum, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu.


Na faɗa muku, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku, kada ku bauta wa gumakan Amoriyawa, waɗanda kuke zaune a ƙasarsu.’ Amma ba ku yi biyayya da maganata ba.”


Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa.


Abin da nake yi ba zai zama laifi ba, Yaushe za ka zo wurina? Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.


Zan cika muhimmin alkawarina, In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.


wato gumakan al'umman da suke kewaye da ku, ko suna kusa da ku, ko suna nesa da ku, daga wannan bangon duniya zuwa wancan,


Kada ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar don kada sa'ad da suke shagulgulan bidi'arsu ga allolinsu, suna miƙa musu hadaya, waninsu ya gayyace ku ku ci abin hadayarsa.


Sai Yakubu ya ce wa iyalin gidansa da dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku kawar da gumakan da suke wurinku, ku tsarkake kanku, ku sāke rigunanku,


Jama'a kuwa suka amsa suka ce, “Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji, har a ce mu bauta wa gumaka.


Ko ma bai cece mu ba, ka sani fa ya sarki, ba za mu bauta wa allolinka, ko kuma mu yi wa gunkin zinariya da ka kafa sujada ba.”


Ko da yake al'ummai suna bin gumakansu, Amma mu za mu bi Ubangiji Allahnmu har abada abadin.


Kada ku yi mugunta domin galibin mutane na yi, kada kuwa ku yi shaidar zur a gaban shari'a don ku faranta zuciyar yawancin mutane, domin kada ku sa a kauce wa adalci.


Sa'an nan sai su kwaso waɗansu duwatsu, su sa su a wuraren da suka ciccire waɗancan. Sai a kawo laka a shafe gidan.


da Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ