Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 23:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sai Joshuwa ya kira Isra'ilawa duka, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, da jarumawansu, ya ce musu, “Yanzu na tsufa, shekaruna sun yi yawa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 sai ya aika a kira Isra’ilawa duka, dattawansu, shugabanninsu, alƙalansu, da manyan ma’aikatansu, ya ce musu, “Na tsufa, shekaruna kuwa sun yi yawa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 23:2
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Joshuwa kuma ya tara dukan kabilan Isra'ila a Shekem, ya kuma kira dattawa, da shugabanni, da alƙalai, da jarumawan Isra'ila. Suka hallara a gaban Allah.


Dawuda ya yi umarni a tara dukan shugabannin Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin ƙungiyoyin da suke bauta wa sarki, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da dukan dukiya da dabbobin sarki, da na 'ya'yansa, da fādawa, da manyan sojoji, da jarumawa, a Urushalima.


Ku tattaro mini dattawan kabilanku da manyanku don in faɗa musu wannan magana a kunnensu, in kuma kira sama da duniya su zama shaida a kansu.


kun dai ga abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan al'ummai duka saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku.


Yanzu Joshuwa ya tsufa ƙwarai, sai Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi, ƙasar da za ku mallaka ta ragu da yawa.


Yanzu ga sarki a gabanku, 'ya'yana maza kuma suna tare da ku. Ni na tsufa, na yi furfura, amma na yi ta kai da kawowa a cikinku tun ina yaro har zuwa yau.


Sarki Dawuda ya tsufa ƙwarai, don haka ko an rufe shi da abin rufa ba ya jin ɗumi.


Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra'ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra'ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali.


Dawuda kuwa ya tattara dukan shugabannin Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ