Sai Saminu ya sa musu albarka, ya ce wa Maryamu uwar Yesu, “Kin ga wannan yaro, shi aka sa ya zama sanadin faɗuwar waɗansu, tashin waɗansu kuma da yawa cikin Isra'ila, Zai kuma zama alama wadda ake kushenta,
Gama akwai jama'a jingim, da yawa kuwa mutanen Ifraimu ne, da na Manassa, da na Issaka, da na Zabaluna, da ba su tsarkake kansu ba, duk da haka sun ci Idin Ƙetarewa ba yadda aka ƙayyade ba. Sai Hezekiya ya yi addu'a dominsu, yana cewa, “Ya Ubangiji mai alheri, ka gafarta wa ko wanne
Da Dawuda ya komo gida domin ya sa wa iyalinsa albarka, Mikal, 'yar Saul, ta fito domin ta tarye shi, ta ce masa, “Ƙaƙa Sarkin Isra'ila ya ɗauki kansa yau? Ya kware darajarsa a gaban barorinsa mata kamar yadda shakiyyai suke yi.”
Eli kuwa yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, ya ce, “Ubangiji ya ba ka waɗansu 'ya'ya ta wurin matan nan a maimakon wanda kuka ba Ubangiji.” Bayan wannan sai su koma gida.
Sa'an nan Sama'ila ya faɗa wa jama'a ka'idodin sarautar. Ya rubuta su cikin littafi, ya ajiye a wuri mai tsarki. Sa'an nan ya sallami jama'a duka kowa ya koma gidansa.
Saul ya zaɓi mutum dubu uku (3,000) daga Isra'ila, dubu biyu (2,000) su zauna tare da shi a Mikmash da ƙasar tuddai ta Betel, dubu ɗaya (1,000) kuma su zauna tare da Jonatan a Gibeya ta Biliyaminu, sauran jama'a kuwa ya sallame su, su koma gida, kowa zuwa alfarwarsa.
A rana ta takwas ya sallami jama'ar, su kuwa suka yabi sarki. Sa'an nan suka kama hanyar gidajensu suna murna, suna farin ciki saboda dukan alherin da Ubangiji ya yi wa bawansa, Dawuda, da jama'arsa, Isra'ilawa.