Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 22:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Za ku kuma daina bin Ubangiji ne yau? Idan kuka tayar masa yau, gobe zai yi fushi da dukan jama'ar Isra'ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Yanzu za ku daina bin Ubangiji ne? “In kuka yi wa Ubangiji tawaye yau, gobe zai yi fushi da dukan mutanen Isra’ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 22:18
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin 'yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama'a saboda zunubin mutum ɗaya?”


“In ji dukan taron jama'ar Ubangiji, ‘Wane irin cin amana ne wannan da kuka yi wa Allah na Isra'ila har da kuka bar bin Ubangiji yau?’ Kun tayar wa Ubangiji yau da kuka gina wa kanku bagade.


Yosiya kuwa ya kawar da dukan abubuwan banƙyama daga dukan ƙasar da jama'ar Isra'ila suke da ita. Ya sa dukan waɗanda suke a Isra'ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu. A dukan kwanakin ransa, ba su kauce daga bin Ubangiji Allah na kakanninsu ba.


Daga lokacin da Amaziya ya bar bin Ubangiji, sai suka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, amma ya gudu zuwa Lakish, sai suka sa a bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi.


Saboda haka Ubangiji ya aiko da annoba a kan Isra'ila. Mutum dubu saba'in (70,000) na Isra'ila suka mutu.


Shaiɗan ya tashi gaba da Isra'ila, sai ya iza Dawuda ya ƙidaya Isra'ilawa.


Sa'ad da Ubangiji ya ɓalle Isra'ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat ya zama sarki. Yerobowam kuwa ya karkatar da jama'ar Isra'ila daga bin Ubangiji. Ya sa su suka aikata babban zunubi.


Amma idan kai, ko 'ya'yanka, kun bar bina, ba ku kiyaye umarnaina da dokokina ba, waɗanda na yi muku, amma kuka tafi, kuka bauta wa waɗansu gumaka, kuka yi musu sujada,


Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa. Ya kuwa zuga Dawuda a kansu, ya ce, “Tafi ka ƙidaya jama'ar Isra'ila da ta Yahuza.”


Sama'ila kuwa ya ce musu, “Kada ku razana, gama kun riga kun aikata wannan mugunta, duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta masa da zuciya ɗaya.


Idan za ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa, ku yi biyayya da maganarsa, ba za ku karya umarnin Ubangiji ba, idan kuma ku da sarkin da yake sarautarku za ku bi Ubangiji Allahnku, kome zai zamar muku daidai.


Lokacin da Akan, ɗan Zera, ya yi rashin aminci cikin abubuwan da aka haramta, ai, dukan Isra'ilawa aka hukunta. Ba shi kaɗai ya hallaka don zunubinsa ba.”


A cikin kayan ganimar na ga wata kyakkyawar alkyabba irin ta Shinar, da shekel dari biyu na azurfa, da sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai na yi ƙyashi, na kwashe su, ga su a binne a ƙasa a alfarwata da azurfa a ƙarƙashi.”


Isra'ilawa sun yi zunubi. Sun ta da alkawarina, wanda na umarce su, gama sun ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, sun sa a kayansu, sun yi ƙarya.


Amma Isra'ilawa suka ci amana, gama Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza ya ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.


Gama za su sa 'ya'yanku su bar bina, su bauta wa gumaka. Wannan zai sa Ubangiji ya husata, ya hallaka ku da sauri.


Musa kuma ya ce wa Haruna, da 'ya'yansa maza, wato, Ele'azara da Itamar, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku kyakketa rigunanku don kada ku mutu, don kada Ubangiji ya yi fushi da taron jama'a duka, amma 'yan'uwanku, wato, dukan Isra'ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya ƙone.


Gama idan kun ƙi binsa, zai sāke yashe ku a jeji. Ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakar mutanen nan duka.”


Da suka zo wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad, ya ce musu,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ