“Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya hutar da jama'arsa, Isra'ilawa, bisa ga yadda ya alkawarta. Daga cikin abin da ya alkawarta duka na alheri ba ko ɗaya da bai cika ba, kamar yadda ya alkawarta wa bawansa, Musa.
domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sākewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu ƙarfafa ƙwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai.
Yanzu Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na tashi a maimakon tsohona, Dawuda, na hau gadon sarautar Isra'ila, kamar yadda ya alkawarta, ga shi kuwa, na gina Haikali saboda Ubangiji Allah na Isra'ila.
Ka iske shi amintacce a gare ka, Ka kuwa yi masa alkawari. Ka yi alkawari za ka ba shi ƙasar Kan'ana, Da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, Da ta Yebusiyawa, da ta Girgashiyawa, Ta zama inda zuriyarsa za su zauna. Ka kuwa cika alkawarinka, gama kai mai aminci ne.