42 Kowane birni yana da wuraren kiwo nasa kewaye da shi.
42 Dukan garuruwan nan kowannensu yana kewaye da wurin kiwo.
Jimillar biranen da wuraren kiwo nasu da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama'ar Isra'ila guda arba'in da takwas ne.
Haka kuwa Ubangiji ya ba Isra'ilawa dukan ƙasar da ya rantse zai ba kakanninsu. Suka ci ƙasar, suka zauna a ciki.