Daga kabilar Biliyaminu aka ba su Geba tare da makiyayarta, da Allemet tare da makiyayarta, da Anatot tare da makiyayarta. Dukan biranen iyalansu guda goma sha uku ne.
Sarki kuma ya ce wa Abiyata, firist, “Ka koma ƙasarka ta gādo a Anatot, gama ka cancanci mutuwa, amma yanzu ba zan kashe ka ba domin ka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji Allah a gaban Dawuda, tsohona, domin kuma ka sha wahala duka tare da tsohona.”