Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 21:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Sai aka ba su Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar tuddai ta Yahuza tare da wuraren kiwo nata da suke kewaye. Arba shi ne mahaifin Anak.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 an ba su, Kiriyat Arba (wato, Hebron), da wurin kiwon da yake kewaye da ƙasar kan tudu ta Yahuda. (Arba shi ne kakan Anak.)

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 21:11
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Rabonsu ya haɗu da Hebron ta yankin ƙasar Yahuza, da makiyayar da suke kewaye da ita.


A kwanakin nan Maryamu ta tashi da hanzari, ta tafi wata ƙasa mai duwatsu, zuwa wani gari na ƙasar Yahuza.


Bayan shekara huɗu sai Absalom ya ce wa sarki, “Ina roƙonka, ka yardar mini in je Hebron in cika wa'adina wanda na yi wa Ubangiji.


Suka kuma tafi su yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a Hebron wadda a dā ake kira Kiriyat-arba. Suka kashe Sheshai, da Ahiman, da Talmai.


da Hunta, da Kiriyat-arba, wato Hebron, da Ziyor, birane tara ke nan da ƙauyukansu.


A dā sunan Hebron Kiriyat-arba ne. Arba kuwa babban mutum ne cikin gwarzayen. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.


Yakubu kuma ya zo wurin mahaifinsa a Mamre, a Kiriyat-arba, wato Hebron ke nan, inda Ibrahim da Ishaku suka yi baƙunci.


sa an nan ta rasu a Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar Kan'ana. Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makoki, yana baƙin ciki domin Saratu.


Zuriyar Haruna tana cikin iyalan Kohatawa waɗanda suke Lawiyawa. Kuri'arsu ce ta fito da farko.


Amma saurukan birnin da ƙauyukansu an ba Kalibu, ɗan Yefunne, su zama mallakarsa.


da Hebron, da dukan wuraren da Dawuda da mutanensa suka taɓa tafiya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ