Yoshuwa 20:9 - Littafi Mai Tsarki9 Waɗannan su ne biranen mafaka da aka keɓe domin dukan Isra'ilawa, da baƙin da suke baƙuntaka cikinsu. Don duk wanda ya yi kisankai ba da niyya ba zai iya tserewa zuwa can don kada ya mutu ta hannun mai bin hakkin jini. Zai zauna a can har lokacin da za a gabatar da shi a gaban taron jama'a. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 In wani mutumin Isra’ila ko kuma wani baƙon da yake zama a cikinsu, ya yi kisankai cikin kuskure, zai iya gudu zuwa biranen da aka keɓe, ba za a bari mai neman ramako yă kashe shi kafin jama’a su yi masa shari’a ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |