Sai mutumin ya ce, “A'a, gama na zo ne kamar sarkin yaƙin rundunar Ubangiji.” Sai Joshuwa ya sunkuyar da kansa, ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada, ya ce masa, “Wace magana ce Ubangiji yake faɗa wa bawansa?”
Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin kakannin gidajen kabilan jama'ar Isra'ila, suka rarraba ta hanyar jefa kuri'a a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada a Shilo. Ta haka suka gama rarraba ƙasar.