Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 2:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Idan waninku ya fita daga ƙofar gidanki zuwa kan titi, to, alhakin jininsa yana bisa kansa, mu kuwa sai mu kuɓuta. Amma idan aka sa wa wani hannu wanda yake cikin gida tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 In wani ya fita kan hanya, alhakin jininsa yă kasance a kansa; ba ruwanmu. Amma in aka taɓa wani da yake cikin gidanki tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 2:19
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

sai Bulus ya ce da jarumin yaki da kuma sojan. “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba yadda za a yi ku tsira.”


Da suka mūsa masa, suna ta zaginsa, ya karkaɗe tufafinsa ya ce musu, “Alhakinku yana a wuyanku! Ni kam na fita. Daga yau wurin al'ummai zan je.”


Gama Ubangiji zai ratsa don ya kashe Masarawa, sa'ad da ya ga jinin a bisa kan ƙofar, da dogaran ƙofa duka biyu sai ya wuce ƙofar, ba zai bar mai hallakarwa ya shiga gidanku, ya kashe ku ba.


Jinin da yake bisa gidajenku zai nuna inda kuke. Sa'ad da na ga jinin zan tsallake ku, ba kuma wani bala'in da zai same ku, ya hallaka ku, a lokacin da zan bugi ƙasar Masar.


To mutumin da ya raina Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka tsarkake shi da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani kuke tsammani ya cancanta fiye da wancan?


a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina ba, wanda ya danganta da bin Shari'a, sai dai da adalcin nan wanda yake tsirowa daga bangaskiya ga Almasihu, wato, da adalcin nan wanda yake samuwa daga Allah ta wurin bangaskiya.


Saboda haka ina dai tabbatar muku a yau, cewa na kuɓuta daga hakkin kowa,


Wanda yake soro, kada ya sauko garin ɗaukar wanda yake a gidansa.


Ubangiji zai ɗora masa alhakin mugayen ayyukansa, gama ya kashe mutum biyu ba da sanin tsohona Dawuda ba, waɗanda kuma suka fi shi adalci, wato Abner ɗan Ner, shugaban sojojin Isra'ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban sojojin Yahuza.


Balle fa ku da kuke mugayen mutane, da kuka kashe adali a gadonsa, a cikin gidansa, ba sai in nemi hakkin jininsa a hannunku ba, in kawar da ku daga duniya?”


Dawuda kuwa ya ce, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe wanda Ubangiji ya keɓe.’ ”


Mutanen kuwa suka ce mata, “Ranmu a bakin naki, idan ba ki tone al'amarinmu ba, za mu yi miki alheri da aminci sa'ad da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”


Mutumin kuma da ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa ke nan, su biyu ɗin za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu.


“Dukan wanda ya zagi mahaifinsa, ko mahaifiyarsa za a kashe shi, gama ya zagi mahaifinsa da mahaifiyarsa. Alhakin jininsa yana wuyansa.


Yanzu fa, ku rantse mini da Ubangiji, kamar yadda na yi muku alheri, haka ku kuma za ku yi wa gidan mahaifina, ku ba ni tabbatacciyar alama.


Amma idan kika tone al'amarin nan namu, to za mu kuɓuta daga rantsuwar da kika rantsar da mu.”


Ku ɗauki tuntun ezob, ku tsoma cikin jinin da yake a kasko, ku yarfa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada kowa ya fita daga gidansa sai da safe.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ