Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 19:50 - Littafi Mai Tsarki

50 Bisa ga umarnin Ubangiji, suka ba shi garin da ya roƙa, wato Timnatsera a ƙasar tudu ta Ifraimu. Ya sāke gina garin, ya kuwa zauna a ciki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

50 yadda Ubangiji ya umarta, suka ba shi garin da ya ce a ba shi, Timnat Serad a ƙasar tudu ta Efraim. Ya kuma gina garin ya zauna a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 19:50
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka binne shi a ƙasar gādonsa a Timnat-sera wadda take cikin karkarar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga'ash.


Suka binne shi a Timnat-sera a ƙasar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga'ash, a ƙasar gādonsa.


'Yarsa kuma ita ce Sheyera, wadda ta gina garin Bet-horon na kwari da na tudu, ta kuma gina Uzzen-sheyera.


Sa'ad da mutanen Isra'ila suka gama rarraba gādon ƙasar, suka ba Joshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikin nasu.


Waɗannan su ne hakimai, da kuma lardunan da suke aiki. Ben-hur yana a ƙasar tudu ta Ifraimu. Ben-deker shi ne mai lura da biranen Makaz, da Shalim, da Bet-shemesh, da Elon-bet-hanan. Ben-hesed shi ne mai lura da Arubot, da Soko, da dukan ƙasar Hefer. Ben-abinadab shi ne mai lura da dukan jihar Dor, ya auri Tafat 'yar Sulemanu. Ba'ana ɗan Ahilud shi ne mai lura da biranen Ta'anak da Magiddo, da dukan jihar Bet-sheyan, kusa da garin Zaretan, kudu da garin Yezreyel, har zuwa birnin Abel mehola da birnin Yokmeyam. Ben-geber shi ne mai fura da birnin Ramot-gileyad, da ƙauyukan Yayir da Manassa, waɗanda suke a Gileyad, da kuma yankin Argob, wanda yake a Bashan, duka dai akwai manyan garuruwa sittin masu garu da ƙyamare na tagulla. Abinadab ɗan Iddo shi ne mai lura da birnin Mahanayim. Ahimawaz shi ne mai lura da Naftali, ya auri Basemat 'yar Sulemanu. Ba'ana ɗan Hushai shi ne mai lura da Ashiru da garin Beyalot. Jehoshafat ɗan Faruwa shi ne mai lura da Issaka. Shimai ɗan Ila shi ne mai lura da ƙasar Biliyaminu. Geber ɗan Uri shi ne mai lura da jihar Gileyad wadda Sihon Sarkin Amoriyawa, da Og Sarkin Bashan, suka mallaka. Bayan waɗannan sha biyu akwai hakimi ɗaya da yake kan ƙasar Yahuza.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ