Sa'ad da Danawa suka rasa karkararsu, suka tafi, suka yaƙi Leshem. Da suka ci ta, sai suka hallaka mutanenta da takobi, suka mallaki ƙasar, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato Dan.
“Ga sunayen kabilan da rabon gādonsu. Yankin Dan, shi ne daga iyakar arewa daga tekun. Ya bi ta Hetlon zuwa ƙofar Hamat, har zuwa Hazar-enan wadda take iyakar Dimashƙu daga arewa, daura da Hamat. Ya zarce daga gabas zuwa yamma.