Amma maimakon Yunusa yă tafi, sai ya gudu daga wurin Ubangiji zuwa Tarshish. Ya tafi Yafa, nan ya sami jirgin ruwa yana gab da tashi zuwa Tarshish, ya kuwa biya kuɗinsa, ya shiga tare da masu jirgin zuwa can don yă tsere wa Ubangiji.
Mu kuwa za mu yanko maka dukan katakan da kake bukata a Lebanon, mu kawo maka su a kan gadajen fito ta hanyar teku, zuwa Yafa, domin ka kwashe ka kai Urushalima.”
Sa'ad da Danawa suka rasa karkararsu, suka tafi, suka yaƙi Leshem. Da suka ci ta, sai suka hallaka mutanenta da takobi, suka mallaki ƙasar, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato Dan.