A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Zimri ya yi sarauta kwana bakwai a Tirza. A lokacin nan sojoji suka kai wa Gibbeton ta Filistiyawa yaƙi.
Ba'asha ɗan Ahija kuwa daga gidan Issaka ya yi wa Nadab maƙarƙashiya, ya kashe shi a Gibbeton ta Filistiyawa, gama Nadab da mutanen Isra'ila sun kewaye Gibbeton da yaƙi.
Aka kuma ba su birane huɗu daga kabilar Dan, wato Elteki tare da wuraren kiwo nata, da Gibbeton tare da wuraren kiwo nata, da Ayalon tare da wuraren kiwo nata, da Gat-rimmon tare da wuraren kiwo nata.