A kwana a tashi, ga matar Yahuza, 'yar Shuwa ta rasu. Da Yahuza ya gama karɓar ta'aziyya, sai ya haura Timna wurin masu sausayar tumakinsa, da shi da abokinsa Hira Ba'adullame.
Sai suka kai akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Amma da aka kai shi Ekron, sai mutanen Ekron suka fashe da kuka, suka ce, “Sun kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra'ila don ya kashe dukanmu.”