Sa'an nan Joshuwa ya yi magana da Ubangiji a gaban Isra'ilawa a ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa gare su, ya ce, “Ke rana, ki tsaya a Gibeyon, Kai kuma wata, ka tsaya a kan kwarin Ayalon.”
Suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, suka ratsa ta ƙasar Shalisha, amma ba su same su ba. Suka kuma bi ta ƙasar Shalim, a can ma ba su same su ba. Sai suka bi ta ƙasar Biliyaminu, amma ba su same su ba.