A kwanakin nan ba sarki a Isra'ila. A wannan lokaci kuwa kabilar Dan suna ta neman yankin ƙasar da za su samu, su zauna. Gama har yanzu ba su sami nasu gādon ƙasa tare da sauran kabilar Isra'ila ba.
“Ga sunayen kabilan da rabon gādonsu. Yankin Dan, shi ne daga iyakar arewa daga tekun. Ya bi ta Hetlon zuwa ƙofar Hamat, har zuwa Hazar-enan wadda take iyakar Dimashƙu daga arewa, daura da Hamat. Ya zarce daga gabas zuwa yamma.
Haka nan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra'ila ya umarta.