Gama Ubangiji ne ya taurara zukatansu har da za su tasar wa Isra'ilawa da yaƙi don a hallaka su, a shafe su ba tausayi, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Wannan shi ne lissafin aikin tilas da sarki Sulemanu ya sa domin ginin Haikalin, da na fādarsa, da kuma Millo, a kuma gina garun birnin. Ya kuma sa tilas a sāke gina garuruwan Hazor, da Magiddo, da Gezer.
Saboda haka suka keɓe Kedesh ta Galili a ƙasar tuddai ta Naftali, da Shekem ta ƙasar tuddai ta Ifraimu, da Kiriyat-arba, wato Hebron, ta ƙasar tuddai ta Yahuza.