Ubangiji kuwa ya ba da su a hannun Isra'ilawa, suka kuwa ɗibge su, suka runtume su, har zuwa Sidon Babba, da Misrefot-mayim, har zuwa gabashin kwarin Mizfa. Suka karkashe su ƙaƙaf.
Birnin Sidon, ke abar kunya ce! Teku da manyan zurfafan ruwaye sun yanke hulɗa da ke, sun ce, “Ban taɓa haihuwar 'ya'ya ba, ban taɓa goyon 'ya'ya mata ko maza ba.”
Yankin ƙasar Kan'aniyawa kuwa ya milla tun daga Sidon, har zuwa wajen Gerar, har zuwa Gaza, zuwa wajen Saduma, da Gwamrata, da Adma, da Zeboyim, har zuwa Lasha.
Ba wanda zai ceci mutanen Layish, gama suna nesa da Sidon, ba su kuma sha'ani da kowa. A kwari guda ne da Bet-rehob. Danawa kuwa suka sāke gina birnin, suka zauna a ciki.